Ƴan Majalisar Wakilan Amurka, sun kada kuri’ar amincewa da karin tallafin dala biliyan arba’in ga Ukraine.
Yawancin ‘yan Republican sun bi sahun takwarorinsu na Democrat wajen goyan bayan yarjejeniyar.
Za a yi amfani da kudaden ne wajen bayar da tallafin soji ga kasar da kuma taimakon jin kai ga fararen hula da mamayar Rasha ta shafa.
Wakilin BBC ya ce tallafin na dala biliyan hudu wanda yan majalisar suka amince da shi da baki guda ya zarta yadda Shugaba Biden ya nema.
A yanzu ya zarce zuwa majalisar dattawa domin amincewa da shi a can ma kafin shugaban kasar ya rattaba masa hannu.