Shugaban Amurka Joe Biden ya ce, zai bai wa Isra’ila duk wani agajin da ya dace bayan wannan kazamin hari da mayakan Hamas suka kai ma ta.
Ya ce shi da kansa zai riƙa magana da Faraministan Isra’ilar Benjamin Natanyahu.
Haka ma Amurkar ta ce tana aiki da gwamnatocin wasu ƙasashe domin yayyafawa rikicin ruwa da kuma tabbatar da cewa bai fantsama ba.
Ƙasashe da dama a Gabas ta Tsakiya cikin har da Masar da Saudiyya da kuma Jordan na magana da juna domin tsara yadda za a kwantar da rikicin.