fidelitybank

Amurka za ta sayarwa da Najeriya makamai masu kai hari

Date:

Amurka ta amince ta sayar wa Najeriya makamai da kudinsu ya kai na dala biliyan daya da zummar karfafa yaki da kungiyoyi masu rike da makamai.

A wata sanarwa da hukumar hadin kai game da tsaro ta Amurka ta fitar, ta ce, Najeriya ta bukaci sayen jiragen masu saukar Ungulu guda 12 masu kai hare-hare da makami, inda aka nufa ba tare da matsala ba.

Amurka ta ce, daga yanzu Najeriya ba za ta fuskanci wata matsala ba wajen sayen makamai daga wurin ta ba.

Sai dai a na sa rai wannan batun zai dauki akalla shekaru biyar kafin a kammala shi, domin kuwa zai hada da horas da dakarun tsaron Najeriya kan yadda za su yi aiki da makaman da kuma kauce wa kai hari kan fararen hula.

Wannan ne karo na biyu da Amurka ke sayar wa Najeriya makamai cikin shekaru biyar.

A baya gwamnatin Barack Obama ta ki sayar wa Najeriya makamai bisa zargin take hakkin dan adam.

Sai dai a shekarar 2017, gwamnatin Donald Trump ta amince ta sayar wa Najeriya jiragen yaki samfurin Super Tucano guda 12.

A shekarar da ta gabata ne aka kai jiragen Najeriya.

today daily post news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp