fidelitybank

Amurka za ta marawa NDLEA baya na yaki da miyagun kwayoyi

Date:

Gwamnatin Amurka ta bayyana aniyarta na yin wani shiri domin ƙarfafa wa hukumar Hana sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta NDLEA, ta hanyar inganta binciken kimiyya da na sinadarai da kuma inganta hanyoyin tattara bayanan sirri.

A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Femi Baba Femi ya fitar ranar Litinin ya ce taimakon na Amurka na zuwa ne bayan da shugaban hukumar Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya ya buƙaci hakan daga hukumomin na Amurka bayan jerin ganawa da ya yi da manyan jami’an Najeriya da na Amurka.

Baya ga taimako a ɓangaren binciken kimiyya da na sinadaran, gwamnatin ta Amurka ta ce shirin zai taimaka wa hukumar wajen samun hanyoyin tattara bayanan sirri ta hanyar na’urori na zamani.

Matakin na zuwa ne bayan da wata ƙungiya mai suna Abdul Samad Rabiu Initiative (ASR Africa) ta bayar da kyautar naira miliyan 500 ga hukumar ta NDLEA domin ɗaukar nauyin wasu manyan ayyukan hukumar.

nigeria news(punch)

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Da yuwar Sojojin mu za su shiga yaƙi don tallafa wa Isra’ila – Trump

Rundunar sojin Isra'ila IDF ta ce ta ƙaddamar da...

Isra’ila ta kai hari cibiyoyin ƙera nukiliyar Iran

Yayin da aka shiga rana ta shida na yaƙi...

Najeriya za ta kwashe ƴan ƙasarta dake zaune a Iran da Isra’ila

Gwamnatin tarayya ta ce, tana kammala shirye-shiryen gaggawa domin...

Makami mai Linzami ya faɗa kan cibiyar tattara bayanan sirrin Isra’ila

Kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Iran ta ce, ƙasar...

Iran ta ƙaddamar da sabbin hare-haren makamai masu linzami kan Isra’ila

Rundunar sojin Isra'ila ta ce, Iran ta ƙaddamar da...

Isra’ila ta na da makaman nukiliya 90

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya dade yana cewa Iran...

Kashe jagoran Iran Ayatullah shi ne kawo ƙarshen rikici – Isra’ila

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce duk wani shiri...

Jerin sunayen masu Fashin Waya 51 da aka kama a Kano

Rundunar ƴansandan Kano, ta fitar da jerin sunayen Mutane...

Iran ta dakatar da tashin jirgi a ƙasarta

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Iran ta...

Poland za ta kwashe dukkannin ƴan ƙasarta daga Isra’ila

Poland na shirin kwashe kusan ‘yan kasarta 200 daga...

Kisan Binuwai abun haushi ne bai kamata a ƙyale ba – Atiku

Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da Kisan Benue, tare...

Ƴan Bindiga sun ajiye makamai a Katsina

Wasu fitattun jagororin ƴanbindiga da suka addabi yankunan ƙaramar...
X whatsapp