Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya ce Amurka za ta kori jakadan Afirka ta Kudu a ƙasar, bayan an zarge shi da nuna ƙiyayya ga Amurka da tsanar shugaba Trump.
A wani saƙo da ya wallafa a shafin X, Mista Rubio ya ce jakadan, Ebrahim Rasool ba shi da sauran dama a Amurka.
A watan da ya gabata, Mista Trump ya katse tallafin da ake bai wa gwamnati a Afirka ta Kudu, bayan ya zargi cewa ƙasar na ƙwace filayen manoma fararan-fata.
Sannan yana nuna jin haushin ƙasar kan kai ƙarar Isra’ila ICC