Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine, ya sanar da cewa, sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken da na harkokin tsaro, Lloyd Austin za su ziyarci birnin Kyiv a wannan Lahadin.
Mista Zelensky ya ce, yana sa ran su iso kasarsa da kayayyakin taimako da Ukraine ke ta roko a kai.
Ya kuma sanar da cewa,kusan mutane rabin miliyan – da suka hada da yara akalla dubu biyar – an maido su daga yankunan Ukraine da Rasha ta mamaye zuwa yankin Rasha.
Mista Zelensky ya kuma soki ganawar da sakataren janar na MDD, Antonio Guterres, zai yi da Vladimir Putin a Moscow a ranar Talata kafin ya je Kyiv.