Ma’aikatar shari’a ta Amurka ta cimma matsaya kan wasu shari’u biyu da suka buƙaci ƙwace wasu manyan kadarori na alfarma da aka samar da su a ƙasar ta hanyar laifukan almundahanar kuɗaɗe.
Wasu takardu daga ma’aikatar shari’ar ƙasar sun nuna cewa batun ya shafi tsohuwar ministar albarkatun man fetur ta Najeriya Diezani Alison-Madueke da wasu abokan kasuwancinta biyu Kolawole Akanni Aluko da Olajide Omokore.
Da wannan mataki a yanzu ma’aikatar shari’ar ƙasar ta ce, ta ƙwace kuɗin da ya kai dala miliyan 53.1, ƙimar kuɗin kadarorin idan aka sayar da su.
Takardun kotun sun nuna cewa daga shekarar 2011 zuwa 2015 Diezani wadda a lokacin take ministar man fetur a Najeriya ta karɓi cin hanci daga abokan kasuwancinta.
Wadda ita kuma Diezani ta riƙa bai wa kamfanoninsu manyan kwangilolin man fetur.
Ma’aikatar shari’ar Amurkan ta ce, an yi amfani da kuɗaden da aka biya a matsayin cin hancin da yawansu ya kai sama da dala miliyan 100, wajen sayan manyan kadarori a Amurka, ciki har da rukunin gidaje a California da New York da kuma Galactica Star.