fidelitybank

Amurka ta yi tur da harin Isra’ila a makarantar Gaza da ya kashe Yara da dama

Date:

Mataimakiyar shugaban ƙasar Amurka, Kamala Harris ta yi Allah-wadai a mamadin fadar White House da kashe fararen hula a Gaza sakamakon mummunan hari ta sama da Isra’ila ta kai kan wata makaranta a jiya Asabar.

Ms Harris, wadda ita ce kuma ƴar takarar shugabar ƙasa a Jam’iyar Democrats a zaɓen da za a yi a watan Nuwamba, ta ce wannan karon ma an sake kashe fararen hula masu yawa, ta kuma sake nanata kira da a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da sako waɗanda aka yi garkuwa da su a Gaza.

Ta ce Isra’ila na da damar kai wa Hamas hari amman ta yi ammanar cewa yana da matuƙar muhimmaci a kiyaye rayukan fararen hula.

Mutum sama da 70 harin na Isra’ila ya kashe a ginin makarantar inda Falasɗinawa da ke gudun hijira suka fake, kamar yadda darektan wani asibiti ya gaya wa BBC.

Kakakin sojin Isra’ila ya ce, makarantar al-Taba’een da aka kai harin na zaman wata cibiya ta aikin soji ta Hamas da kungiyar Islamic Jihad, zargin da Hamas ta musanta.

legitnewsnigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Tarzomar kama baƙin haure a Amurka na yamutsa hazo

An shiga rana ta uku a tarzomar da ake...

Alhazai sun kammala aikin Hajji bana

A ranar Lahadin da ta gabata ne alhazai miliyan...

Tinubu gyaran ƙasa za ka mayar da kai ba zaɓen 2027 ba – ACF

Ƙungiyar Tuntuɓar Juna ta Arewacin Najeriya, ta yi kira...

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...
X whatsapp