Amurka ta yi Allah-wadai da sace yara ‘yan makaranta a jihar Kaduna.
Rahotanni na cewa, kimanin mutane 200 da suka rasa matsugunansu, wadanda suka kunshi mata, maza da mata ne, wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka yi garkuwa da su, a lokacin da suke cikin dazuzzuka domin diban itace a yankunan Gomboru-Ngala da karamar hukumar Dikwa a jihar Borno.
Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya a shafinta na X ya bukaci gwamnatin Najeriya da ta kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika tare da tabbatar da sun fuskanci sakamakon da zai biyo baya.
“Amurka ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan sace ‘yan makaranta da aka yi a Kaduna da kuma ‘yan gudun hijira a Borno.
“Zuciyarmu tana kan iyalan wadanda abin ya shafa. Muna tsayawa tare da ku wajen neman wadanda suka aikata laifin su fuskanci shari’a kuma a gaggauta dawo da duk wadanda aka kama.
“Muna goyon bayan kokarin Najeriya na ganin an sako su,” in ji ta.


 

 
 