Sojojin Amirka sun ce sun kai hare-hare ta sama wurare biyu da sojin juyin-juya-hali na Iran ke amfani da su a Syria.
A wata sanarwa da sakataren tsaron Amirka ya fitar Lloyd Austin, ya bayyana hare-haren na tsantsar kare kai.
Sama da mako guda da rabi kenan da sojin Amirka ke zafafa kai hare-hare kan kungiyar masu dauke da makamai da Iran ke marawa baya.
Sun ce martani ne kan hare-haren da suke addabar sojin Amirka da ke Iraqi da Syria hare-hare.
Ma’aikatar tsaro ta Pentagon ta ce an kai wa kawancen da Amirka ke jagoranta a Iraqi da Syria hari sama da sau 16 cikin wannan watan, daidai lokacin da ake zaman dar-dar a yankin gabas ta tsakiya saboda yakin Isra’ila a Gaza