fidelitybank

Amurka ta yabawa Kenya yadda ta yi zaɓe

Date:

Ofishin jakadancin Amurka a Kenya ya yaba wa ‘yan kasar Kenya saboda yadda aka gudanar da zabe cikin lumana, sannan ya bukaci dukkan jam’iyyun siyasar kasar da su hada kai su yi aiki tare domin warware dukkan abubuwan da ke damun kasar cikin sauki.

Ofishin ya ce ayyana William Ruto a matsayin wanda ya ci zaben shugaban kasa kuma abu ne mai matukar muhimmanci a siyasar kasar.

Kazalika ofishin ya bukaci shugabannin siyasar kasar da su ci gaba da jan hankalin magoya bayansu a kan zama lafiya da kuma kaucewa dukkan wata fitina.

An ayyana Mr Ruto a matsayin wanda ya samu nasara a zaben shugaban kasar da aka yi inda ya samu 50.9 cikin 100 a kudin da aka kada abin da ya sa ya kayar da abokin takararsa tsohon Firaiminista Raila Odinga.

Wakilan Mr Odina a wasu mazabun sun ba za su iya tabbatar da sahihancin zaben ba sannan kuma wasu Kwamshinonin hukumar zaben sun sanar da sakamakon zaben da ba su tabbatar da sahihancinsa ba.

Mr Ruto ya yi alkawarin aiki tare da ‘yan kasar yana mai cewa sakamakon zaben an yi shi cikin adalci.

An rinka shagulgula bayan sanar da sakamakon zaben, yayin da rahotanni kuma ke cewa an samu barkewar zanga-zanga a wasu yankunan da ke da magoya bayan Mr Odinga. In ji BBC Hausa.

legit.ng.news.

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

APC ta yi kwaf daya a zaben cike gurbin Kaduna da Jigawa

Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Jigawa ta yi...

Ba mu yarda da zaben Ghari da Tsanyawa ba – NNPP

Jam'iyar NNPP mai mulkin jihar Kano a arewacin Najeriya...

QPC ta nemi INEC ta soke zaɓen Kano

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta nemi hukumar zaɓe...

Zaɓen Kano: An kama Mutane 288 da tayar da zaune tsaye

Rudunar ƴansandan jihar Kano, ta sanar da kama mutum...

An Kama wakilin jam’iyya da Naira miliyan 25.9 na Siyan Kuri’a

Jami’an tsaro sun kama wani da ake zargin wakilin...

Farashin kayan abinci na rugu-rugu a Najeriya – NBS

Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta ce hauhawar farashin...

Kotun Kano ta ce a kamo mata Dagacin Tamburawa

Kotun Shari’ar Musulunci da ke shelkwatar Hisbah a Kano,...

Kotu ta ƙwace motocin gwamnatin Zamfara guda 40 daga hannun Matawalle

Kotun Daukaka Kara da ke a Sokoto ta tabbatar...

A na cigaba da gudanar da zaben cike gurbi harda Kano

Kano na ɗaya daga cikin jhihohin da ake kaɗa...

Mutane 12 sun mutu a wani hatsari a Kano – FRSC

Hukumar Kiyaye Haddura ta Ƙasa (FRSC) reshen Kano, ta...

Masarutar Rano ta haramta aurar da Yaran da ba su kammala karatun Firamare ba

Masarautar Rano a Kano ta haramta cire yarinya daga...

Matatar Dangote za ta fara jigilar mai kyauta ga gidajen mai

Matatar man Dangote za ta fara jigilar mai kyauta...
X whatsapp