Ƙasashen Rasha da Ukraine sun amince da tsagaita wuta a yaƙin da sojojin ruwansu ke yi a tekun Bahar Aswad, a wasu yarjejeniyoyi daban-daban da suka cimma da Amurka.
An cimma hakan ne bayan tattaunawa na tsawon kwana uku a ƙasar Saudi Arabia.
A wata sanarwa Amurka tace duka ɓangarorin za su ci gaba da ƙoƙarin ganin an cimma zaman lafiya mai ɗorewa, lamarin da zai sake buɗe muhimmiyar hanyar da ake bi don kasuwaci.
Sannan sun sha alwashin inganta matakai don aiwatar da abubuwan da aka cimma a baya da suka shafi haramta kai wa juna hari kan cibiyoyin makamashi. A cewar fadar White House.
Sai dai Rasha ta ce tsagaita wutar zata fara aiki ne bayan an janye mata wasu takunkuman da aka ɗora mata kan cinikayyan abinci da kuma taki.
Shugaba, Volodymyr Zelensky na Ukraine ya yaba da tsagaita wutar na Bahar Aswad a matsayin abu ne da ya dace.
Tawagogin Rasha da na Ukraine dai basu zauna a teburin tattaunawa guda ba a Riyadh, sai dai jami’an Amurka ne ke tattaunawa da kowane ɓangare daban.