Ma’aikatar tsaron Pentagon ta ce, ta ƙara tura dakaru da jiragen yaƙin Amurka, zuwa Gabas ta tsakiya, yayin da ake zaman ɗar-ɗar a yankin.
Iran da ƙawayenta sun sha alawashin mayar da martani kan Isra’ila na kisan shugaban Hamas a Tehran da kwamandan Hizbollah a Beirut.
Wani mai gabatarwa a gidan talabijin Iran, ya ce, nan da wasu sa’o’i masu zuwa duniya za ta ga abun mamaki.