Ministocin harkokin wajen ƙasasashen Larabawa da ke taro a Jordan, sun shaida wa sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken cewa akwai buƙatar gaggauta tsagaita wuta a Gaza.
Takwaransa na Jordan, Ayman Safadi, ya ce Isra’ila na aikata laifukan yaƙi inda take ƙoƙarin dulmuya Gaza cikin tekun ƙiyayya, da za a ɗauki gwamman shekaru ba a manta da shi ba.
Sai dai Mista Blinken ya jaddada musu cea Amurka na son ganin an tsagaita wutar.
Ya ƙara da cea Amurka amince da batun tsagaita wuta da kare farar hula da shigar da agaji, da fitar da marasa lafiya.
Mista Blinke ya ce ya yi magana da shugabannin Isra’ila kan hakan, sai dai ya ce burinsu shi ne kawar da Hamas.