Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya, ya taya al’ummar jihar Osun murnar zaben gwamnoni da aka gudanar a ranar 16 ga watan Yuli.
Ofishin Jakadancin ya ce: “Mun yaba da hadin kan ma’aikatan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da jami’an tsaro wadanda suka taimaka wajen samar da ingantaccen tsari wanda ke nuna muradin al’umma.
“Muna kira ga dukkan ‘yan Najeriya da su yi rajista don kada kuri’a a yanzu domin a ji muryar ku a zaben kasa da na jihohi a 2023.”