Amurka ta soki yadda Isra’ila ke yaƙi a zirin Gaza, a daidai lokacin da aka shiga watanni biyu da ɓarkewar yaƙin tsakaninta da Hamas.
Sakataren harkokin wajen Amurka ya ce Isra’ila ba ta cika alƙawarin da ta ɗauka na kare farar hula a yaƙin da ta ke ƙara zafafawa a Gaza ba, idan aka kwatanta da halinda ake ciki a yanzu.
Anthony Blinken ya shaidawa manema labarai a Washington cewa, akwai matakai da dama da Isra’ila ya kamata ta ɗauka domin tabbatar da cewa Falasdinawa Farar hula sun isa tudun mun tsira cikin nutsuwa.
Mr Blinken ya ce ba wai kawai su isa wurare masu aminci kaɗai ba, har da yi musu bayanin inda ya kamata su nufa, da lokacin da za su tafi, suna buƙatar abubuwa kamar ruwan sha da abinci da magani.
Babban jami’in Majalisar Ɗinkin Duniya, Martin Griffiths ya ce yana fatan buɗe iyakar Isra’ila da Kerem Shalom ka iya sauƙaƙa kai kayan agaji cikin sauri ga Falasdinawa. In ji BBC.