Gwamnatin Amurka ta dauki matakin sauya wa dakarunta de ke ƙasar Nijar matsuguni bayan juyin mulkin da aka yi a ƙsar.
Mai magana da yawun ma’aikatar tsaro ta Pentagon Sabrina Singh ta ce a mayar da wasu sojojinta da ke sansani na 101 da ke kusa da babban birnin kasar Yamai zuwa sansaninta na 201 da ke Agadez “a matsayin riga-kafi” makonni shida bayan da sojoji suka karɓi mulkin ƙasar.
Misis Singh ta ce wata ƙaramar tawagar sojojin za su ci gaba da zama a sansanin Yamai.
Bayan juyin mulkin da sojoji sukayi a watan Yuli, Amurka ta dakatar da wasu ayyukan agajin da kasashen ketare ke bai wa ƙasar tare da dakatar da horar da sojoji, inda aka killace sojoji a sansanonin.
A hukumance Amurka ba ta kira mamayar da sojoji suka yi a Nijar a matsayin juyin mulki ba, matakin da zai takaita irin taimakon tsaro da Washington za ta iya bai wa kasar da kayayyakin aiki da za a iya turawa ga sojojin.
“Tsarin mu a Nijar bai canza ba. Matsayinmu har yanzu shi ne. Muna fatan za a nemi mafita ta hanyar diflomasiyya, amma babu wata barazana ga jami’an Amurka ko tashin hankali a kasa,” in ji Ms Singh.
Amurka na da a kalla dakaru 1,100 a sansanoninta guda biyu a Nijar.
Sansanin jirage marasa matuka na Agadez mai nisan kilomita 920 daga birnin Yamai.
Ita ma ƙasar Faransa wadda ta kasance tsohuwar ƙasar Nijar ta mulkin mallaka na da dakaru kusan 1,500 a ƙasar.
Sai dai ya zuwa yanzu, Paris ta yi watsi da kiraye-kirayen da shugabannin da suka yi juyin mulki suka yi na su fice daga kasar, lamarin da ya haifar da zanga-zanga yayin da jama’a suka yi sansani a kusa da sansanin.


