fidelitybank

Amurka ta sallami dan kasar Saudiyya daga magarkamar Guantanamo

Date:

Wani dan Saudiyya da Amurka ke tuhuma da zama mutum na 20 ciin wadanda suka kai harin 11 ga watan Satumbar 2001 ya shaki iskar ‘yanci bayan da aka sake shi daga gidan yarin Guantanamo Bay, inji ma’aikatar tsaro ta kasar.

Amurka ta saki Mohammed al-Qahtani, mai shekara 46 kuma ta tasa keyarsa zuwa Saudiyya bayan da wani kwamiti ya sake duba batunsa, kuma ya ce babu alamar zai sake zama mai hatsari ga Amurka.

Kwamitin ya jingina sakamakon nasa ne kan abin da ya kira “tabarbarewar lafiyar kwakwalwarsa”.

Bayan da aka kama shi a a 2001 Amurka ta azabtar da shi har ta kai ga ba za a iya gurfanar da shi a gaban shari’a ba. In ji BBC.

Jamai’an gwamnatin Amurka sun ce dama an shirya cewa, Qahtani zai shiga jirgin United Airlines mai lamaba 93 ne, wanda shi ne ya fado a jihar Pennsylvania bayan da wasu wadanda ake tuhuamr ‘yan al Qaeda ne su hudu suka kwace shi daga matukansa a ranar 11 ga watan Satumbar 2001.

Sai dai Amurka ta hana shi bizar shigga kasar a watan Agustan wannan shekarar.

ng news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp