Amurka ta sanya dala miliyan biyar a matsayin lada ga duk wanda ya taimaka mata wajen kama jagoran ‘yandaba a kasar Haiti.
Ana zargin Jimmy Cheriziyai, wanda aka fi sani da Barbecue, da haddasa rikicin da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba miliyoyi da muhallansu da yunwa.
Jagoran dabar ya mamaye tare da iko da kusan kashi 95 cikin 100 na Port au Prince babban birnin kasar, abin da ya jefa birnin cikin wani hali na rashin bin doka da oda tun bayan kissan tsohon shugaban kasar a 2021.
Masu gabatar da Æ™ara a Amurka na tuhumar Cheriziyai da laifin hada baki da wasu wajan karya takunkuman da Amurka ta sanya wa kasar ta hanyar neman kudade daga ‘yan Haiti mazauna Amurka.
Wakilin BBC ya ce an tura wa Cherizaiyi da kudin wanda ya yi amfani da shi wajan biyan ‘yandabarsa tare da sayan makamai ta haramtaciyyar hanya.
Lauyoyin sun ce kungiyarsa ta G9 ce ke da alhakin aiwatar da ayyukan cin zarafi da suka hada da kisan kai, da fyade, da kuma garkuwa da mutane.