Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5 ga Shirin Abinci na Duniya (WFP) domin samar da tallafin abinci da na abinci mai gina jiki ga ‘yan Najeriya, musamman ma waɗanda rikice-rikice suka raba da muhallansu.
Wannan tallafi zai bai wa WFP damar kai agajin abinci da kula da lafiyar gina jiki ga mutum 764,205 a yankunan Arewa maso Gabas da Arewa maso Yammacin Najeriya da rikici ya shafa.
A cewar shirin, daga cikin masu amfana akwai mata masu juna biyu da masu shayarwa 41,569, da kuma yara 43,235, waɗanda za su karɓi tallafin abincin.
Shirin ya ce wannan taimako daga gwamnatin Amurka na da matuƙar muhimmanci wajen ceto rayuka da rage matsalar yunwa da rashin abinci mai gina jiki a yankunan da rikici ya daɗe yana addaba.