Amurka ta sanya takunkumi kan kamfanoni uku na Rasha da wasu ‘yan kasuwa biyu da take zargi da taimakon Koriya ta Arewa sake inganta makaman nukiliyarta.
Matakin na zuwa ne kwana ɗaya bayan Amurkar da Koriya ta Kudu sun sanar da cewa Arewa ta yi gwajin makami mai linzami wanda ya saba haramcin da Majalisar Dinkin Duniya ta sanya mata.
Hukumomin Amurka sun ce ‘yan tsirarun kamfanoni da ‘yan kasuwar da ke taimakon Koriya ta Arewa da suka fito daga birnin Vladivostok na kasar Rasha suna da makudan kudade.
Gwamnatin Shugaba Biden ta kira gwajin a matsayin tsantsar takalar fada da rashin son zaman lafiya, yayin da Pyongyang ta ce gwajin wani bangare ne na inganta tauraron dan Adam na leken asiri.