Amurka ta ce ta ƙaddamar da wasu sabbin hare-hare kan sansanonin ƴantawayen Houthi da ke ƙasar Yeman.
Wannan shi ne hari da Amurka ta kai mafi girma tun bayan komawar Donald Trump kan karagar mulki a wannan shekarar.
Aƙalla mutum 23 rahotanni suka ce an kashe a Sanaa da arewacin Lardin Saada.
Shugaba Donald Trump ya yi gargaɗin cewa Amurka za ta ci gaba da kai farmaki har sai mayaƙan Houthin sun daina kai wa jiragen ruwan ƙasar hari.