fidelitybank

Amurka ta harbo wani jirgi a sararin samaniyarta

Date:

Amurka ta ce tana ƙoƙarin tattara tarkacen wani abu mai kama da jirgi da ba a san asalinsa ba, bayan da ta harbo shi kan tekun Arctic.

Abin wanda aka ce ya kai girman ƙaramar mota, yana shawagi ne a sama kuma ana ganinsa a matsayin barazana.

A yanzu dai babu wani abu da ya nuna cewa abin da aka harbo din yana aikin sa ido ne.

Wani kakakin Pentagon bai yi wa yan jarida ƙarin bayani ba, game da inda jirgin ya fito ko ma maƙasudin kasancewarsa a sararin samaniyar Amurka.

Ministar tsaron Canada Anita Anand ta ce za su taimaka wajen tura jiragen da za su bi diddigi.

An dai fara ganin abun ranar Alhamis da daddare, to sai dai jami’ai ba su bayyana lokaci ba.

Hakan na zuwa ne mako guda bayan da Amurkan ta harbo wani balan-balan ɗin ƙasar China da aka zarga da leƙen asiri, da aka gani yana shawagi a sararin samaniyar Amurkan. In ji BBC.

sspdf news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp