Amurka a karon farko ta ƙaƙaba takunkumi kan shugaban Cuba, Miguel Diaz-Canel, saboda rawar da ya taka a abin da ta kira cin zalin da gwamnatin Cuban ta aikata wa jama’arta.
Yanzu dai shugaban da wasu masu riƙe da manyan muƙamai ba za su iya shiga Amurka ba.
A martanin da ya yi cikin fushi, ministan harkokin wajen Cuba Bruno Rodriguez ya ce Amurka ba za ta iya karkatar da buƙatun al’ummar Cuba ko ma shugabannin ta ba.
Sanarwar da sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya yi na zuwa ne yayin da aka cika shekara huɗu da ganin zanga-zanga mafi girma da aka yi a tsibirin inda har aka cafke ɗaruruwan mutane.