fidelitybank

Amurka ta haramta amfani da TikTok a ƙasar ta

Date:

TikTok ya bayyana cewa zai ‘daina aiki’ a Amurka daga ranar Lahadi, matuƙar dai gwamnatin shugaba Joe Biden ba ta ɗauki matakin hana dakatar da shi ba.

Hakan na zuwa ne bayan Kotun ƙolin ƙasar, a ranar Juma’a ta amince da matakin Majalisar dokokin Amurka na haramta ayyukan manhajar, har sai idan kamfanin da ya mallaki manhajar – wanda ke da alaƙa da China – ya amince zai sayar da ita ga wani kamfanin Amurka, bisa dalilai na tsaro.

Fadar shugaban Amurka ta White House ta ce ba za ta bayar da umarnin amfani da dokar ba, to amma TikTok ya ce idan har da gaske ne to ya kamata gwamnati ta fitar da sanarwa domin tabbatar wa kamfanonin Apple da Google matsayar tata.

Donald Trump, wanda za a rantsar a matsayin shugaban Amurka a ranar Litinin – ya nuna aniyar ganin ba a tabbatar da haramcin amfani da mahajar ba.

Majalisar Dokokin Amurka ce ta yanke shawarar haramta TikTok a ƙasar ne bisa dalilai na tsaro, inda ta ce akwai yiwuwar gwamnatin China na amfani da manhajar wajen tattara bayanan mutanen Amurka, wanda take amfani da shi wajen yaɗa manufa.

legit news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnan Kano ya kori mataimansa na musamman kan belin Danwawu

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da...

Tsohon Minista a mulkin Buhari ya mutu

Allah ya yi wa tsohon ministan noma da raya...

Kashi 70 na yankin Bukuyum ta Kudu na ƙarƙashin ƴan Bindiga – Ɗan majalisa

Rahotanni daga yakin ƙaramar hukummar Bukuyum na jihar Zamfara...

Goodluck ya fi dacewa ya zama dan takara a 2027 – Lamido

Tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya ce Tsohon...

An gargadi al’umma su yi taka tsan-tsan da ambaliyar ruwan sama

Yayin da ake ci gaba da fuskantar saukar ruwan...

Gwamnatin Tarayya za ta gina hanyar sufurin jirgin ƙasa a Kano

Gwamnatin Tarayya ta ce, za ta samar da titin...

Abin da ya sa muke ci gaba da tsare Sowore – Ƴansanda

Kwamishinan ƴansanda mai kula da sashen kai ɗauki na...

INEC za ta bai wa ɗaurarru damar kaɗa ƙuri’a a lokacin zaɓuka

Hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta ta duba yiwuwar bai...

Mai ya jawo Matan Zamfara su ka yi zanga-zanga

Ɗaruruwan mata ne tsofaffi da masu shawarya suka gudanar...

Aƙalla mutane 24,000 ne suka ɓata saboda Boko Haram a Najeriya

Kungiyar Agaji ta Red Cross ta bayyana cewa aƙalla...

‘Yansanda ku gaggauta sakin Sowore – Obi

Tsohon ɗan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Peter...

PDP ta gargaɗi mambobinta kan goyon bayan Tinubu

Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP a Najeriya ta gargaɗi...
X whatsapp