Amurka ta fitar da wani gargaɗi ga ‘yan ƙasarta da ke zaune a Najeriya da su kauce wa zuwa manyal otal-otal a ƙasar.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwar gaggawa da ƙasar ta aike wa ‘ya’yanta mazauna Najeriya ranar Juma’a 3 ga watan Nuwamba.
Sanarwar gargaɗin ta ce ta an ɗauki matakin gargaɗin ne saboda samun bayanan sirri game da yiwuwar kai hari manyan otol-otal a faɗin ƙasar.
Ta buƙaci Amurkawan da ke ƙasar su riƙa lura a manyan otal-otal, da wuraren da suke zaune, su kuma rage bayyana kansu a bainar jama’a, sannan su riƙa bin shawarwarin tafiye-tafiye zuwa Najeriya da Amurkan ke fitar wa kafin su shiga kowane Otal.
Sanarwar ta ce, “Gwamnatin Amurka na sane da sahihan bayanai da ke nuna barazana a man’yan otal-otal a manyan biranen Najeriya”.
“Jami’an tsaron Najeriya na aiki tuƙuru, don magance barazanar”, in ji sanarwar.
haka kuma sanarwar ta fitar da wasu lambobin wayar ofisoshin jakadancinta da ke Abuja da Legas, ga duk Ba’amurken da ke buƙatar taimako.