Shugaba Biden na Amurka ya gargadi China kan irin abin da zai same ta muddin ta goyi bayan Rasha a yakin Ukraine, sai dai bai fito fili ya bayyana hukuncin ba.
Mista Biden ya furta hakan ne a lokacin da suka yi tattaunawa ta bidiyo ta kusan sa’a biyu da takwaran nasa na China, Xi Jinping, inda ganawar ta kasance ta farko da shugabannin biyu suka yi, tun bayan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.
Manufar Shugaba Biden a wannan tattaunawa dai ita ce, ya san inda China ta karkata a wannan rikici.
Amurka ta fito fili ta nuna abin da take son China ta yi, cewa ta kasance a bangaren da ya kasance daidai na tarihi, wato ta bi sahun masu sukar mamayar da Rasha ta yi wa makwabciyar ta Ukraine.