fidelitybank

Amurka ta gano China ta yaɗa cutar Korona da gangan a duniya

Date:

Hukumar leƙen asiri ta Amurka, CIA, ta gabatar da sabon bayani kan binciken da ta yi game da abin da ake ganin ya haddasa annobar Korona (Covid19) a duniya, inda ta ce tana ganin zai fi yuwuwa ƙwayar cutar ta fita ne daga ɗakin bincike na kimiyya saɓanin daga jikin dabbobi.

Kakakin hukumar ya ce bisa ga dukkan alamu ɓullar cutar na da alaƙa da aikin bincike -maimakon a ce haka kawai ta ɓulla, kamar yadda rahoto ya nuna.

To amma kuma hukumar ta CIA ta ce ba ta da cikakken ƙwarin gwiwa a kan hakan.

Shawarar fitar da wannan sakamako ta kasance ɗaya daga cikin matakan da sabon shugaban hukumar ta CIA, John Ratcliffe, wanda Donald Trump ya naɗa ranar Alhamis, ya yi.

Daman tun a lokacin Trump na farko Ratcliffe, wanda a lokacin darekta ne a hukumar samar da tsaro ga shugaban ƙasa, yana da ra’ayin cewa cutar ta ɓulla ne daga ɗakin kimiyya na cibiyar binciken kimiyya ta Wuhan da ke China.

Cibiyar tana da tazarar tafiyar minti 40 ne a mota daga kasuwar da ake sayar da kifi da sauran naman ruwa – inda ake cewa daga kasuwar ne cutar ta ɓulla.

China dai a kullum tana watsi da zargin cewa ƙwayar cutar ta fita ne daga ɗakin kimiyya, inda take danganta hakan da haramben siyasa na Amurka.

legits news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An sake mayar da yan Najeriya 294 gida daga Nijar

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya Nema ta...

An gano motoci 35 da aka sace a wata shida

Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa a Najeriya ta ce...

Shugaban Laberiya ya je ta’aziyyar Buhari a Monrovia

Shugaban Ƙsaar Laberiya Joseph Nyuma Boakai ya kai ziyarar...

Rundunar Yansandan Kaduna ta hana gangamin goyon bayan Peter Obi

Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta hana gudanar...

Iran ta zartar da hukuncin kisa a kan Mutane 3

Hukumomi a Iran sun zartar wa mutum uku hukuncin...

Ƴansanda sun kama ƙasurgumin ɗanbindiga a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna ta ce, jami'an ta sun...

Sudan ta Kudu ta yi ta’aziyyar Buhari

Mukaddashin Ministan Harkokin Wajen Sudan ta Kudu, Ambasada Akuei...

Trump ya na fama da cuta mai kumbura kafa da toshewar hanyar jini

A ranar Alhamis ne Fadar White House ta sanar...

Yadda aka gudanar da addu’o’in Buhari a Villa

A ranar Alhamis ne aka gudanar da addu'o'i ga...

Rasha tarnaki ce a wajen Tarayyar Turai – Jamus

Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya shaidawa BBC cewa...

Amurka ba ta goyon bayan Isra’ila a harin Syria – Trump

Amurka ta ce ba ta goyon bayan hare-haren da...

Tinubu zai zo Kano ta’aziyyar Dantata

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu zai kai ziyara Kano yau...
X whatsapp