Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya tattauna da hambararren shugaban Nijar Mohamed Bazoum domin jaddada goyon bayansa ga zababbiyar gwamnati.
Ya jaddada cewa “gwamnatin farar hula da aka zaba ita ce hanya mafi dacewa da za ta taimaka wa Nijar zama abokiyar tafiya a fannin tsaro da ci gaban yankin,” in ji kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka, Matthew Miller.
Tun a ranar 26 ga watan Yuli, aka kifar da gwamnatin Bazoum, kuma sojoji na ci gaba da tsare shi tare da iyalansa.
Amurka “na kira a sako shi tare da duk wadanda aka kama ba bisa ka’ida ba, tun bayan da sojoji suka kwace mulki,” in ji Miller.
Sojoji karkashin jagorancin Janar Abdourahmane Tchiani, sun ce za su mika mulki hannun gwamnatin farar hula a cikin shekara uku, amma kungiyar Ecowas ta ki amincewa da wannan bukata.
Kungiyar Ecowas na kokarin sasantawa da shugabannin mulkin soja da suka yi juyin mulki kuma sun yi gargadin cewa idan diflomasiyya ta ki aiki, to za a iya tura dakaru zuwa Yamai.