Amurka ta bayar da umurnin fara kwashe wasu ƙananan ma’aikatanta wadanda ba a bukatar aikinsu cikin gaggawa tare da iyalansu daga Najeriya saboda barazanar kai hari.
Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ne ya tabbatar da hakan a bayanan da yake wallafawa na shawarwari game da ƴan kasar mazauna Najeriya, a ranar Talata.
Sanarwar ta ce ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja ba zai iya samar wa ‘yan kasar mazauna Najeriya taimakon gaggawar da suke bukata ba, haka kuma ayyuka sun yi wa karamin ofishin da ke birnin Legas yawa.