Rahotanni daga kafofin yaɗa labaran Amurka sun bayyana cewa, a yau Masar ta buɗe iyakarta da Gaza zuwa wani lokaci domin barin a shigar da kayan agaji da kuma ficewar ƴan ƙasashen waje daga yankin.
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ba ta tabbatar da rahotannin ba.
Wani sako da aka wallafa a shafin sada zumunta, ya bai wa Amurkawa da ke Gaza shawarar cewa su matsa kusa da iyakar Rafah idan suka tabbatar babu wani haɗari.
A ranar Lahadi ne sakataren harkokin wajen Amurkan Antony Blinken, ya kai ziyara Masar domin shawo kan jami’an ƙasar a kan su bude iyakar Rafah.


