Shugaban kasar Amurka, Joe Biden, ya sanar da bayar da tallafin biliyoyin daloli, domin ciyar da Afirka gaba a yayin taron shugabanin kasashen Afirka da ke gudana a Washington.
“Amurka za ta zage dantse kan ci gaban Afirka,” a cewar shugaba Biden da yake sanar da shugaban kasashen Afirka 40 da suka halarci taron.
Haka kuma ya bayyana aniyar Amurka ta ci gaba da karfafa dangantakarta da Afirka, inda ya sanar da bai wa kasashen tallafin dala biliyan 55 a matsayin sabon tallafi ga Nahiyar na tsawon shekaru uku. Ciki har da dala miliyan 100 na samar da makamashi.
Ya sanar da mahalarta taron cewar idan Afirka ta yi nasara, haka ma Amurka.
Mr Biden ya yi jawabi kan muhimmancin shugabanci na gari, samar da jama’a mai koshin lafiya da makamashi mai sauki.
Ana kallon taron shugabanin kasahen Afirka da ke gudana a Amurka a matsayin wani yunkuri ne kasar na ganin ta dawo da karfin ikon ta kan Nahiyar a daidai lokacin da China, Rasha da Turkiya ke fadada damarsu a nahiyar.
Wannan ne karo na farko a shekaru takwas da Amurka ta karbi bakunci irin wannan taro.