Shugaba Joe Biden ya tabbatar da cewa Amurka za ta taimakawa Ukraine da makaman roka da na atilari na zamani, abin da ta dade ta na roko a yakin da ta ke yi da mamayar Rasha.
Mista Biden da ya wallafa jawabin a Jaridar New York Times, ya ce makaman za su bai wa Ukraine damar maidawa Rasha martani.
Makaman da akai wa lakabi da HIMARS, su na cin dogon zango idan an harba su.
Wakilin BBC ya ce, an kara ware tallafin dala miliyan 700 ga sojin Ukraine, wanda za a kaddamar a yau Laraba.
Makaman masu cin dogon zangon da ya kai kilomita 80, jami’an Amurka sun ce, sun amince da bai wa Ukraine makaman rokar, bayan samun tabbaci daga shugaba Volodymr Zelensky kan ba za a yi amfani da su domin farwa Rasha ba.