Amurka ta aike da wani jirgin sama mai sayan magunguna domin kwashe babban jami’in Binance Holdings Limited, Tigran Gambaryan daga Najeriya.
An kwashe Tigran Gambaryan bayan da gwamnatin Najeriya a ranar Laraba ta yi watsi da tuhumar da ake yi masa na halasta kudaden haram.
Mai ba da shawara kan harkokin tsaro na Amurka, Jake Sullivan ya bayyana cewa sakin Gambaryan ya faru ne sakamakon tattaunawa da ‘yan Najeriya da jami’an Amurka, a cewar jaridar New York Times.
“Wani jirgin sama sanye da kayan aikin likita ya tashi daga Abuja babban birnin Najeriya don dawo da shi Amurka don samun kulawar da ake bukata,” in ji shi.
An kama babban jami’in na Binance ne a wata ziyarar aiki da ya kai Najeriya a watan Fabrairu, kuma an tsare shi a gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja tun a watan Afrilu.
A ranar Laraba, 23 ga Oktoba, 2024, hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya ta yi watsi da tuhumar da ake wa Gambaryan.