Shugaban Amurka Joe Biden, yua kaddamar da wani shiri na cire ƙasashen Uganda da Gabon da Nijar da kuma Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya daga cikin shirin bunƙasa kasuwanci na musamman tsakanin Amurka da Afirika da aka fi sani da ‘African Growth and Opportunity Act (AGOA)’.
Shugaban ya ce dalilin da ya sa aka yanke wannan shawarar shi ne, ko dai waɗannan ƙasashe sun shiga cikin jerin manyan kasashe da ke take haƙƙin ɗan’adam ko kuma ba su nuna ci gaba a mulkin dimokraɗiyya ba.
AGOA, wani shiri ne da aka ƙaddamar a cikin 2000, da ke bai wa ƙasashen Afirka na kudu da hamadar Sahara damar shiga ba Amurka ba tare da biyan haraji ba, da kayayyaki sama da 1,800.
Shugaba Biden ya ba da misali da rashin bin tsarin siyasa da bin doka da oda a matsayin dalilan rashin cancantar Nijar da Gabon, saboda juyin mulkin da sojoji suka yi a baya-bayan nan.
Ya kuma yi nuni da gagarumin take hakkin ɗan’adam da gwamnatocin kasashen Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Uganda suka yi a matsayin hujjar cire su daga cikin shirin.
Ya zuwa yanzu dai babu wani martani a hukumance daga ƙasashen hudu da abin ya shafa.
Wannan matakin ya biyo bayan korar da aka yi wa Burkina Faso da Mali da kuma Guinea daga AGOA bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a waɗannan kasashe.