fidelitybank

Amurka na binciken yadda takardun sirri na shirin Isra’ila na kai wa Iran hari

Date:

Amurka na gudanar da bincike kan wasu muhimman takardu na sirri da suka fito fili, waÉ—anda ke bayyana nazarin da Amurka ke yi na shirin Isra’ila na kai wa Iran hari, kamar yadda Shugaban majalisar wakilan Amurkar Mike Johnson ya tabbatar.

Rahotanni sun ce a makon da ya wuce ne aka wallafa takardun a intanet, inda aka ce suna bayyana wasu hotunan tauraron É—an’Adam da ke nuna yadda Isra’ila ke jigilar makamai a shirin da take yi na kai harin ramuwar-gayya na harin makami mai linzami da Iran ta kai mata ranar 1 ga watan Oktoba.

Takardun waÉ—anda aka bayyana a matsayin babban sirri – Æ™asashe biyar Æ™awayen Amurka – Birtaniya da Kanada da New Zealand da kuma Australia na iya musayarsu a tsakaninsu, kamar yadda kafar yaÉ—a labarai ta CBS, da ke Amurka wadda ke alaÆ™a da BBC ra ruwaito.

Tsawon makonni Isra’ila ke duba lokaci da kuma yadda za ta kai wa Iran wannan hari – abin da ministan tsaron Isra’ilar ya yi gargaÉ—in cewa zai kasance mai muni kuma na ban mamaki da yankan shakku.

A ranar Juma’a ne aka wallafa takardun da aka danganta da hukumar nazarin bayanan sirri na kasa na Amurka da kuma hukumar tsaron kasar ta Amurka, a wani shafin sada zumunta da muhawara na Telegram da ke da alaÆ™a da Iran.

Sai dai hukumomin Amurka da Isra’ila da ke da alaka da lamarin ba su fito fili sun ce komai ba game da lamarin.

Amurka na gudanar da bincike kan ko da niyya wani jami’in leken asirinta ya fitar da takardun ko satarsu aka yi ta hanyar kutsen intanet.

nigeria news(punch)

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp