A lokacin da yake amsa tambayoyin ‘yan jaridu, sakataren harkokin tsaron Amurka, Anthony Blinken a taron ƙasashe bakwai masu ƙarfin tattalin arziki na duniya, ya shaida wa ‘yar jaridar BBC, Jessica Parker cewa Amurka ba ta da hannu a hare-haren da Isra’ila ta kai wa kasar Iran a daren Juma’a.
Sai dai kuma ya ce sun ƙudirin niyyar bai wa Isra’ilar duk wata kariya da take buƙata “kamar yadda kuka gani a baya-bayan nan.”
Sai dai kafofin yaɗa labaran Iran da jami’ai sun rage kaifin rahotannin wani hari da aka kai kan wurare daban-daban a birnin Isfahan da Tabriz.
Hossein Dalirian, kakakin hukumar kula da sararin samaniyar Iran, a shafinsa na X ya ƙaryata labarin harbo makami mai linzami kai tsaye daga wajen ƙasar abin da ya sha banbam da bayanan jami’an Amurka cewa makami mai linzami na Isra’ila ya kai hari kan Iran.