Nan gaba a yau Amurka da Tarayyar Turai za su kara saka wa Rasha sabbin takunkumai a matsayin martani kan zargin aikata laifukan yaki da Ukraine ke yi wa sojin Rasha kan kisan fararen hula a garin Bucha.
Sakatariyar yaɗa labaran fadar White House, Jen Psaki, ce ta sanar da hakan a wajen taron manema labarai.
“Ku sa ran za a sanya takunkumin kan jami’an gwamnatin Rasha da iyalansu, da kamfanoni, da haramta zuba jari da ɗora alhakin duk abin da ya faru a kan jami’an Rasha,” in ji ta.
Mujallar Wall Street Journal ta rawaito cewa, Amurka na duba yiwuwar sanya wa babban bankin Rasha Sberbank takunkumi.