Ministar kudi ta Amurka, Janet Yellen, ta ce an samu kyaututuwar dangantaka tsakanin ƙasarta da China a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata.
Ta bayyana hakan ne da safiyar Lahadi a birnin Beijing, a karshen ziyararta ta kwana huɗu a Chinar.
A jiya Asabar, Yellen ta shafe sa’o’i da dama tana tattaunawa da sabon babban mataimakin firimiyan ƙasar a kan harkokin kuɗi He Li-Feng.
Idan aka yi la’akari da yadda danganataka take tsakanin ƙasashen Amurka da China to ko ba komai za a iya cewa alla san barka game da waɗannan kalamai. A cewar BBC.
A don haka ne ma ganin irin yadda alakar take tsakanin ƙasashen biyu a baya, sakatariyar ta tunatar da cewa ‘’ba wata ziyara daya da za ta iya magance kalubalen da ke tsakaninsu, dare daya’’
To amma ta ce wannan ziyara za ta taimaka wajen ginawa da samar da wata managarciyar hanyar sadarwa da sabbin masu rike da akalar harkokin tattalin arzikin China.
A jiya Asabar ne Misis Yellen ta yi ganawarta ta farko keke da keke da mataimakin Firimiya He Lifeng, zaman da aka ce ya dauke su sa’a shida.