A wata sabuwar sanarwa da Hamas ta fitar, ta ce, Amurka ce ke da ”alhakin kisan gillar’ da aka yi a Gaza bayan da ta bayyana cewa Isra’ila ta shaida wa Amurka shirinta na kai hare-haren gabanin kai harin.
Sanarwar ta ce hakan ya ”tona asirin ƙaryar da suke yi na ikirarinsu kan damuwa da kawo ƙarshen yaƙin”.
”Muna buƙatar ƙasashen duniya su ɗauki matakin gaggawa na kama masu aikata laifukan yaƙi da masu goya musu baya” in ji Hamas.
A gefe guda kuma kafar yaɗa labarai da ke da alaƙa da Hamas, mai suna Filastin, ta ce an kashe jam’ian gwamnatin Hamas huɗu a hare-haren Isra’ila.
Hazalika shugaban hukumar lafiya da Hamas ke jagoranta, Munir al-Barsh ya ce mutane fiye da 660 aka jikkata a hare-haren, kuma wasu da dama na ƙarƙashin ɓaraguzai.