Jagoran Iran Ayatollah Ali Khamenei, ya ce kasar Amurka ita ce musabbabin jefa kasar Ukraine cikin rudani a yakin da suke da Rasha.
A cikin wani jawabi a talabijin na kasar Ayatollah ya taɓo batun yaƙin Rasha a Ukraine.
A cikin jawabinsa ya ce “Ukraine ta faɗa tarkon manufofi rikici na Amurka. Muna goyon bayan kawo ƙarshen yaƙi a Ukraine, amma maganin ko wane rikici shi ne a gano tushensa. Amurka ce, tushen rikici a Ukraine,” in ji Khamenei.