Shugabar majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi ta ce Amurka ba za ta ƙyale China ta mayar da barazana da kuma fin ƙarfin da take nunawa kan Taiwan ya zama tamkar wani abin da ba aibu ba.
Ms Pelosi ta fadi hakan ne bayan da China ta kammala atisayen soji na murza gashin baki, da ta yi a matsayin martani ga ziyarar Pelosin zuwa tsibirin.
Ta dai ce ta je Taiwan ne domin nuna goyon bayan ga yadda take tafiyar da harkokinta na demokradiyya tare da nuna cewar China ba ta isa ta kebance tsibirin ba.
Dan majalisa Gregory Meeks na cikin tawagar da ta je Taiwan din, ya kuma shaida wa BBC cewar ba sa da-na-sanin ziyarar ta Pelosi.
Ya ce ‘yan Taiwan ne suka gayyace mu, shugaba da kuma mutanen Taiwan na son mu je, ba za mu juya wa abokanmu baya ba.


