Shugabar majalisar wakilan Amurka, Nancy Pelosi, ta ce, Amurka ba za ta lamunce wa China ta hantari Taiwan ba, bayan ziyarar da Ms Pelosi din ta kai ta fusata China.
Lokacin da ta yi magana a birnin Tokyo, na kasar Japan, Pelosi ta ce ba manufar ziyararta a kasashen Asia ba ne ta sauya matsayin da kasashe suke a kai ba.
Yanzu haka dai sojojin China na gudanar da gagarumin atisaye a kusa da Taiwan, a matsayin martani kan ziyarar.
Wakiliyar BBC ta ce, Ms Pelosi ita ce ‘yar siyasar Amurka mafi girman mukami da ta ziyarci Taiwan cikin shekaru 25, kuma ta yi watsi da zargin cewa, wani kokari ne na bayar da kariya ga tsibirin.
China na kallon Taiwan a matsayin mallakinta, kuma tana iya yin amfani da karfi domin mayar da ita cikin ikonta, matukar bukatar hakan ta tashi.


