Amurka ta ce ba ta goyon bayan hare-haren da Isra’ila ta kai a Syria a cikin wannan makon.
Isra’ila dai ta yi ruwan bama-bamai a babban birnin Damascus da kuma lardin Sweida da ke kudancin kasar, inda suka sake kai hare-haren da yammacin jiya Alhamis.
Ba kasafai ne ake ganin irin wannan rashin jituwa tsakanin Isra’ila da Amurka a ƙarƙashin gwamnatin Trump ba.
Ba a dai tabbatar da ko Shugaba Trump ya nuna ɓacin ransa kan hare-haren a tattaunawar tarho da suka yi da Firaminista Netanyahu a jiya Alhamis ba.