Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, ya ce, ƙasarsa ba ta da masaniya ko kuma hannu a kisan da aka yi wa Isma’il Haniyeh jagoran siyasar Hamas.
Sakataren harkokin wajen Amurkan, ya ce, ba zai iya cewa ga abin da lamarin ke nufi ba, amma ya jaddada muhimmancin samun tsagaita wuta a Gaza.
Shi kuwa firaiministan Qatar, wadda ke shiga tsakani a tattaunawar tsagaita wutar da ake, ya ce, mutuwar Mr Haniyeh za ta iya kawo cikas a tattaunawar da ake.
Tuni dai Rasha da China da kuma Turkiyya suka yi alawadai da kisan da aka yi wa Ismail Haniyeh, inda shugaba Erdogan na Turkiyya ya ce, an yi hakan ne da nufin karya lagon Falasdinawa.
Kasar Iran ta ce, akwai buƙatar su yi alwadai da wannan ta’addanci da aka yi, sannan sun sanar da Isra’ila cewa, al’ummar Iran ba za ta taba bari a kashe mata bako a kasar kuma su yi shiru ba.
An kashe shugaban harkokin siyasa na ƙungiyar Hamas Ismail Haniyeh a Iran, jim kaɗan bayan ya halarci bikin rantsar da sabon shugaban ƙasar, Masoud Pezeshkian.


