Tobi Amusan ta kasa kare kambunta na gasar tseren mita 100 na mata a gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta Afirka ta 2024 sakamakon rashin lafiya.
Mai rike da tarihin duniya na da burin lashe lambar zinare ta uku a jere a gasar.
Amusan ta zo kan gaba a gasar tseren mita 100 na mata a shekarar 2018 a Asaba da kuma shekaru biyu da suka gabata a Mauritius.
Idan da ta fafata kuma ta yi nasara, da Amusan ta bi sahun Maria Usifo da Glory Alozie a matsayin ‘yan wasa tilo da ke da kambun Afirka uku a jere a gasar tseren mita 100 na mata.
Tuni dai Adaobi Tabugo ta Najeriya ta tsallake zuwa wasan karshe.
Tawagar Najeriya ta lashe lambobin zinare biyu a karon farko a gasar a ranar Juma’a.