Ƙungiyar kare hakkin ɗan’adam ta Amnesty International ta yi zargin cewa fararen hula kusan 10,000 ne suka mutu a hannun sojojin Najeriya, tun bayan fara yaƙi da ƙungiyar Boko Haram a arewa maso gabas.
Shugaban ƙungiyar ta Amnesty a Najeriya, Isa Sanusi, wanda ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Maiduguri, ya kuma zargi Boko Haram da sojoji da laifukan take ƴancin ɗan’adam.
A cewarsa, dakarun soji sun take ƴancin bil’adama yayin gudanar da ayyukansu a yankin na arewa maso gabas. In ji BBC.
Ya nuna takaicinsa kan yadda sojoji suka musanta hannunsu a lamarin bayan gabatar musu da rahoton da Amnesty ta yi kafin ta fitar da shi ga jama’a.
Sanusi ya ce tuni ƙungiyar ta shigar da ƙara gaban Kotun Duniya da ke Hague, kan zargin take ƴancin ɗan’adam a arewa maso gabas.