Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta yi Allah wadai da ci gaba da tsare wani fitaccen mai amfani da shafukan sada a Najeriya mai suna Ghali Isma’ila da aka fi sani da Sultan kan zargin yaɗa wani bidiyo kan ‘lafiyar’ shugaba Tinubu.
A ƙarshen makon da ya gabata ne aka kama Sultan tare da tsare shi kan zargin da Amnesty ta bayyana da maras tushe.
Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ta ce kamun da hukumar DSS ta yi wa matasahin ɗan asalin jihar Kano ya saɓa wa doka.
Amnesty ta kuma zargi jami’an DSS da zuwa gidan yarin da aka tsare Sultan tare da tilasta masa ba su lambobin sirrin buɗe wayoyinsa da na shiga shafukan sada zumuntarsa (Password) ba tare da tuntuɓar lauyoyinsa ba.
Ƙungiyar ta Amnesty ta ce hakan ya saɓa wa ƴancinsa na tsare sirri da ƴancin faɗar albarkacin baki.
Amnesty ta kuma soki yadda hukumomin Najeriya ke kamawa tare da razana masu amfani da shafukan sada zumunta wajen hana su bayyana ra’ayinsu.
Daga ƙarshe ƙungiyar ta yi kira ga hukumomin na Najeriya su gaggauta sakin matashin ba tare da wasu sharuɗɗa ba.