Ƙungiyar kare hakkin ɗan’adam ta duniya, Amnesty International ta yi Alla-wadai da kama wasu matasa da suka fita don tun waɗanda aka kashe lokacin zanga-zangar EndSars.
Jami’an ƴansanda sun yi dirar miƙiya kan matasan waɗanda suka taru a Lekki toll gate yau Lahadi.
Matasan sun ce sun fita domin tuna mutanen da aka kashe a watan Oktoban 2020 lokacin zanga-zangar adawa da cin zalin ƴansandan Sars.
An ruwaito cewa matasan sun taru ne da misalin karfe 8 na safe a Lekki toll gate riƙe alluna da kuma kwalaye ɗauke da rubuce-rubuce da dama.
Wata sanarwa da ƙungiyar Amnesty ta fitar, ta ce ba za a lamunci abin da jami’an ƴansandan jihar Legas suka yi ba.
“Muna Allah-wadai da kakkausar murya kan abin da ƴansandan Najeriya suka yi kan mutanen da suka fita a Lekki toll gate domin tunawa da masu zanga-zangar lumana da aka kashe yayin zanga-zangar EndSars a Oktoban 2020. Ba za mu amince da amfani da hayaki mai sa hawaye ba da kuma kame,” in ji ƙungiyar ta Amnesty a wani sako da ta wallafa a shafin X.