fidelitybank

AMNESTY ta gaggauta janye kalaman ta a kan mu ko mu dauki mataki – Rundunar ‘Yansanda

Date:

Rundunar ‘yan sandan kasar nan, ta buƙaci Kungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International a Najeriya, da ta gaggauta janye kalaman da ta wallafa na zargin jami’an tsaro da aikata laifukan cin zarafin masu zanga-zanga,

Ta kuma buƙaci ƙungiyar ta nemi afuwar al’umma.

A cewar kakakin rundunar Muyiwa Adejobi, ya ce an riga an aike wa ƙungiyar wasikar tun a ranar shida ga wannan watan na Janairu, kuma muddin ba ta aiwatar da wannan buƙata ba, rundunar ƴan sandan za ta ɗauki matakin shari’a

Bayanin da rundunar ta fitar ya nuna cewa akwai abubuwa da dama da suka haɗa zarge-zargen da rundunar ƴan sandan ta ce na ƙarya ne, masu nasaba da take hakkin ɗan Adam ta hanyar azabtar da masu zanga-zanga.

Bayanin ya ce akwai hujjoji ƙarara da suka nuna babu wani abu makamancin haka da ya wanzu, ciki kuwa har da hotunan bidiyo da gidajen talabijin suka watsa kai tsaye a lokacin da ake gudanar da zanga-zangar ta watan Agustan shekarar 2024, kuma rundunar ƴan sandan ta yi nazarin ƙwaƙwaf tare da gudanar da bincike inda ta gano dukan abubuwan da kungiyar ta yi iƙirari ba su da ƙamshin gaskiya.

A cewar rundunar ƴansandar Najeriyar, jami’anta sun yi amfani da ƙwarewa tare da bin cikakkun ka’idojin aikin da aka san jami’an tsaro da su, har ma a wuraren da suka fuskanci farmaki daga masu zanga-zanga bai sa sun yi amfani da ƙarfin da ya wuce kima ba.

legit news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp